Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tsawaita wa'adin mika mulki zai sake kasancewa a tsakiyar tattaunawar da mahukuntan rikon kwarya na kasar Mali. M. Jonathan zai gana da wakilan Tarayyar Afirka, da na ECOWAS da kuma na Minusma, sai kuma jami'an diflomasiyya da ke Bamako babban birnin Mali. A karshen watan Disamba, hukumomin rikon kwarya na kasar Mali sun ba da shawarar yin shekaru biyar, don aiwatar da sauye-sauye da dama kafin shirya zabe.
342/